Wani mutum ya gabato daga mutanen kauye ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - dan ya nuna masa aikin da zai shigar da shi aljanna, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya amsa masa da cewa shiga aljanna da tsira daga wuta sun tsaya akan bada rukunan Musulunci, na bautar Allah Shi kadai, kuma kada ka hada wani abu da Shi. Ka tsaida salloli biyar din Allah Ya wajabta su akan bayinSa a kowanne yini da dare. Ka bada zakkar dukiyar da Allah Ya wajabtasu akanka, ka bada su ga wadanda suka cancanta l. Ka kuma kiyaye akan azimin watan Ramadan a lokacinsa. Sai mutumin ya ce na rantse da wanda raina yake a hannunSa ba zan kara komai akan aikin da aka wajabta ba wanda na ji shi daga gareka na ayyukan da'a ba, kuma ba zan rage ba daga garesu ba. Lokacin da ya juya (ya tafi) sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Wanda yake son ya yi duba zuwa ga wani mutum daga 'yan aljanna to ya yi duba zuwa ga wannan balaraben kauyen.