Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi addu'a da ni'ima da farin ciki da kyau a duniya, kuma Allah Ya isar da shi zuwa ni'imar aljanna da ni'imarta a lahira; ga wanda ya ji zancensa sai ya haddace shi har ya isar da shi ga waninsa, sauda yawa wanda aka isarwa hadisin ya zama ya fi kiyayewa kuma ya fi fahimta kuma ya fi ikon yin istinbaɗi daga wanda ya ruwaito hadisin, sai na farkon ya zama yana kyautata hadda da dakkowa, na biyun kuma ya zama yana kyautata fahimta da istinbaɗi (tsamo hukunci).