Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kamanta yana mai ban ammaki wanda yake anfanuwa da abinda ya zo da shi na hujjoji da kuma hanyar da zata kai zuwa ga abin da ake nema, da kuma ilimi na shari'a da ƙasar da ruwa mai yawa yake sauka a ita; sai ta zama ta kasu kaso uku: Na farkonsu: Tsarkakakkiyar ƙasa mai tsarki, wacce take karɓar ruwan sama, sai ta tsirar da tsirrai mai yawa ɗanye da busasshe, sai mutane suka amfana da ita. Na biyunsu: Ƙasar da take riƙe ruwa, saidai ba ta tsirar da shuka, ita tana kiyaye ruwa dan mutane su amfana da shi; sai su sha su shayar da dabbobinsu da kuma shukarsu. Na ukunsu: Ƙasa madaidaiciya mai santsi wacce ba ta riƙe ruwa kuma ba ta tsirar da shuka, ita akan kanta ba ta amfana da ruwan da hakan ba, haka kuma mutane basu amfana da ruwan ba. Haka nan masu jin abinda aka aiko Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da shi na ilimi da kuma shiriya. Na farko: Malami wanda ya fahimci Addinin Allah, mai aiki da iliminsa, mai sanar da waninsa; shi a matsayin ƙasa ce mai tsarki wacce ta sha ruwa sai ta amfana ita akan kanta, kuma ta tsirar sai ta amfani waninta. Na biyu: Mai haddace ilmi sai dai ba shi da fahimta da kuma istinbaɗi, shi ya tara ilimi, ya dilmiyar da lokacinsa a cikin hakan, sai dai cewa shi bai yi aiki da nafilfilinsa ba, ko bai fahimci abinda ya tara ba; to shi ala ce ga waninsa, kuma a matsayin ƙasa ce wacce ruwa ba ya tabbata a cikinta ballantana mutane su amfana da shi. Na uku: Wanda yake jin ilimi ba ya haddace shi, ba kuma ya aiki da shi, kuma ba ya ciratarsa ga waninsa; to shi a matsayin ƙasar gishiri ce ko ƙasa mai santsi wacce babu tsirrai a cikinta kuma ba ta karɓar ruwa ko tana ɓata shi ga waninta.