Mu'awiya Dan Abu Sufyan - Allah Ya yarda da su - ya fito ga wata halƙa a cikin Masallaci, sai ya tambayesu akan wanne abu ne suka taru? sai suka ce: Muna ambatan Allah, sai ya sa suka rantse, Allah Ya yarda da shi - cewa su ba su yi nufin komai da taruwarsu ba sai zikiri, sai suka rantse masa, Sannan ya ce da su: Lallai ni ban rantsar da ku ba dan tuhuma gareku da kuma kokwanto a gaskiyarku ba, sannan ya bada labari game da matsayinsa ga annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kuma cewa shi babu wani mutum dake da matsayin kusancin sa daga gare shi; dan kasancewar Ummu Habiba 'yar uwarsa ce kuma matar annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ce-, dan kuma kasancewarsa daga marubutan wahayi, tare da hakan to shi mai ƙarancin riwaya ne ga hadisai. Sai ya zantar da su cewa annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fito wata rana daga gidansa, sai ya samesu a zaune a cikin masallaci, suna anbaton Allah suna gode masa akan shiryar da su da ya yi , ya kuma ni’imta su da shi, sai - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tambaye su ya kuma rantsar da su da irin abinda Mu'awiya - Allah Ya yarda da shi - ya aikata tare sahabban sa. Sannan annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya faɗa musu sababin tambayar sa gare su da kuma rantsar da su da ya yi: Cewa mala'ika Jibrilu - aminci ya tabbata a gare shi - ya zo masa sai ya ba shi labarin cewa Allah - mai girma da ɗaukaka - Yana yi wa mala'iku alfahari da ku, kuma yana bayyanar da falalarku gare su, kuma yana nuna musu kyakkyawan ayyukanku, Yana yabon ku a gurin su.