An ambatawa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - wasu mutane biyu ɗayansu mai ibada ne, ɗayan kuma malamai ne, wanene yafi a cikinsu? Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Falalar masanain ilimummukan shari'a mai yin aiki da su kuma mai koyar da su akan mai yin ibada wanda ya kaɗaita ga ibada tare da da cewa ya san abinda ya wajaba akansa na ilimi kamar falalarsa ne - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da kuma ɗaukakarsa akan mafi koma baya daga cikin sahabbai Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya bayyana sababin hakan da cewa Allah - tsarki ya tabbatar maSa -, da mala'ikunSa cikin maɗauka al'arshi, da waɗanda ke cikin sammai na sauran mala'iku, da ma'abota ƙasa na aljanu da mutane da dukkanin dabbobi, har tururuwa a gidanta a cikin ƙasa, har kifin da ke cikin kogi; dan ya haɗa dabbobin sarari (tudu) da kogi, dukkanin waɗannan sunayin addu'a ta alheri ga wanda yake koyar da mutane ilimummukan Addinin da a cikinsu akwai tsiran mutane da kuma rabautarsu.