Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tambayi Ubayyu Dan Ka'ab game da mafi girman aya a cikin littafin Allah, sai ya yi kai kawo a amsa, sannan ya ce: ita ce Ayatul Kursiyyi: {Allah babu wani abin bautawa da gaskiya sai Shi, Rayayye tabbatacce da kanSa}, sai Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya karfafashi, kuma Annabi ya daki kirjinsa dan nuni zuwa cikarsa da ilimi da hikima, kuma ya yi masa addu'a da ya tsira da wannan ilimin kuma ya sawwaka masa shi.