Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -yana bayyana cewa idan wani abu ya yi kai-kawo a cikin cikin mai sallah, sai ya rikitar da shi; shin wani abu ya fita daga gareshi ko a'a? to, kada ya fita daga sallarsa ya yanketa don sake alwala, har sai ya tabbatar da samun karin da ya ɓata alwalarsa; ta hanyar ya ji karar tusa, ko ya ji wari; domin abin aka tabbatarw to kokwanto ba ya ɓata shi, shi tabbas ya tabbatar da tsarki (alwala) kari kuma akwai kokwantone a cikinsa.