Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa tunkuɗewa kai da wasu cuta yana wajaba gargwadon nau'o'inta da yadda ta bayyana, baya halatta ga wani ya cutar da kansa ko waninsa daidai wa daida. Kuma ba ya halatta gare shi ya rama cuta da cuta; domin cuta ba a tunkuɗeta da cuta sai dai ta hanyar ƙisasi ba tare da wuce gona da iri ba. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya bayyana narko da faruwar cuta ga wanda yake cutar da mutane, da kuma faruwar wahala ga wanda yake tsanantawa mutane.