explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa tunkuɗewa kai da wasu cuta yana wajaba gargwadon nau'o'inta da yadda ta bayyana, ba ya halatta ga wani ya cutar da kansa ko waninsa daidai wa daida. Kuma ba ya halatta gare shi ya rama cuta da cuta; domin cuta ba a tunkuɗeta da cuta saidai ta hanyar ƙisasi ba tare da wuce gona da iri ba.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Hani game da ramuwa da sama da abin da aka yi.
  • Allah bai umarci bayainsa da wani abu da zai cutar da su ba.
  • Hadisin ƙa'idace mai girma a haramcin cuta, cutarwa kuma tana kasancewa ne da magana ko aiki ko da barin (yin abu).
  • Daga ƙa'idojin shari'a akwai: "Cuta ana gusar da ita", shari'a ba ta tabbatar da cuta, kuma tana inkarin cutarwa.