explain-icon

Bayani

Aliyu Dan Abu Dalib - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa ya kasance da yawan maziyyi yana fita daga gare shi - shi wani ruwa ne fari siriri mai zuba yana fita daga gaba a yayin sha'awa ko kafin jima'ai -. Bai san me zai aikata ba idan ya fita ba, sai ya ji kunyar ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -; domin cewa shi mijin Fadimatu ne 'yar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, Sai ya bukaci Mikdad Dan Aswad ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da hakan, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya amsa masa da ya wanke gabansa sannan ya yi alwala.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Falalar Aliu Dan Abu Dalib - Allah Ya yarda da shi -, yadda kunya ba ta hana shi barin tambayaba ta hanyar (wani).
  • Halaccin wakilci a neman fatawa.
  • Halaccin mutum ya baiwa wani labarin abinda yake jin kunyar shi domin wata maslaha.
  • Najasar maziyyi, da wajabcin wanke shi daga jiki da tufafi.
  • Fitar maziyyi yana daga abubuwa masu bata alwala.
  • Wajabcin wanke gaba da maraina dan zuwansa a wani hadisin daban.