Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana wanda ya yi nufin biyan buƙatarsa na fitsarine ko bayan gida ya fuskanci alƙibla wajen Ka'aba, kuma kada ya juya mata baya, ya sanyata a bayansa; kai ya wajaba akansa ne ya juya ɓangaren gabas ko yamma idan alƙiblarsa kamar alƙiblar mutanen Madina ce. Sannan Abu Ayyub - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa su lokacin da suka je Sham sun samu banɗakunan da aka tanada dan biyan buƙata a cikinsu an gina su suna fuskantar Ka'aba, sun kasance suna juyawa alƙibla baya da jikkunasu, tare da hakan suna neman gafarar Allah.