Daga Salman - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Mushirikai suka ce mana: Lallai cewa ni ina ganin abokin nan naku yana koya muku (abubuwa) har yana koya muku biyan buƙata, sai ya ce: Eh, Lallai cewa shi ya hana ɗayanmu ya yi tsarki da (hannun) damansa, ko ya fuskanci alƙibla, kuma ya yi hani daga (tsarki) da toroson dabbobi ko ƙasusuwa kuma ya ce: «‌Kada ɗayanku ya yi tsarki da ƙasa da duwatsu uku». Ingantacce ne - Muslim ne ya rawaito shi
explain-icon

Bayani

Salman al-Fasrsi - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Mushrikai suka ce mana, suna masu izgili: Lallai Annabinku yana koya muku kowane abu, har yana koya muku ta yaya zaku biya buƙatarku ta fitsari ko bahaya! Salman ya ce: Eh, ya sanar da mu ladubban biyan buƙata; daga cikin hakan cewa shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hanamu mu yi tsarki da hannun dama bayan biyan buƙata dan kiyaye shi daga najasa da kuma girmamawa, ko mu fuskanci Ka'aba a lokacin yin fitsari ko bahaya, kuma ya yi hani daga yin tsarkin hoge da toroson dabbobi da kuma ƙasusuwansu, kuma wanda ya yi kari (hadasi) kada ya wadatu a tsarkin hoge da ƙasa da duwatsu uku.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Bayanin gamewa da kuma cikar Shari'ar Musulunci a cikin dukkanin abinda mutane suke buƙatuwa zuwa gare shi.
  • Bayanin wasu daga cikin ladubban bayan gida da kuma tsarki.
  • Haramcin fuskantar alƙibla a lokacin fitsari ko bahaya; saboda faɗinsa: "Ya hana mu", kuma asali a cikin hani shi ne haramci.
  • Hani daga tsarkin ruwa, ko tsarkin hoge da hannun dama; dan girmama shi.
  • Fifita hannun dama akan na hagu; domin hannun hagu ana amfani da shi ne dan gusar da najasa da kuma ƙazanta, (hannun) dama kuma ga abinda ba haka ba.
  • Wajabcin kawar da najasa da ruwa ko duwatsu, daidai ne najasar kaɗan ce ko da yawa ce.
  • Hani daga tsarkin hoge da ƙasa da duwatsu uku; domin cewa ƙasa da duwatsu uku basa tsarkakewa a galibi.
  • Dukkanin abinda zai sa a samu tsarkakewa da shi to ya isar, kaɗai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya nassanta duwatsu ne; domin sune galibin, wanda kuwa ya zama kamar haka to ba shi da wani abin fahimta.
  • An so tsarkin hogen ya zama witiri (mara), idan tsarkakewar ta tabbata da huɗu to an so ya ƙara na biyar haka nan dai; saboda faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: (Wanda zai yi tsarkin hoge to ya yi shi witiri (mara)).
  • Hanin yin tsarkin hoge da toroson dabbobi; domin cewa shi: Kodai ya zama najasa, ko kuma domin shi abincin dabbobin aljanu ne.
  • Hanin yin tsarkin hoge da ƙashi; domin cewa shi kodai najasa ne, ko kuma domin cewa shi abincin aljanu ne su da kansu.