Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita -: Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya fito daga bayan gida yana cewa: "Ina neman gafararKa".
Ingantacce ne - Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya fito daga biyan buƙatarsa na bayan gida yana cewa: Ina roƙonKa (gafararKa) ya Allah.
Daga Cikin Fa idodin Hadisin
An so faɗin: "Ina neman gafafarKa" bayan fitowa daga wurin biyan buƙata.
Neman gafarar da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi ga Ubangijinsa a dukkanin halaye.
An ce: A cikin sababin neman gafara bayan biyan buƙata: Don taƙaitawa ne a cikin godiyar ni'imomin Allah masu yawa , daga cikinsu akwai sawwaƙa fitar abinda yake cutarwa, kuma ina neman gafararKa dan na shagalta daga anbatanKa a lokacin biyan buƙata.