Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana sashin huklunce-hukuncen tsarki, daga cikinsu: Na farko: Cewa wanda zai yi alwala to ya wajaba akansa ya shigar da ruwa a cikin hancinsa da numfashi, sannan ya fitar da shi ta numfashi kuma. Na biyu: Cewa wanda ya yi nufin tsarkake kazanta mai fita daga gareshi da gusar da ita ba tare da ruwa ba kamar duwatsu da makancinsu to tsarkakewarsa ta zama akan adadin mara mafi karancinsa uku, mafi yawa wanda zai kawar da abinda ya fita zai kuma tsarkake wurin. Na uku: Cewa wanda ya farka daga baccin dare kada ya shigar da tafinsa a cikin kwarya dan ya yi alwala har sai ya wankesu sau uku a wajen kwaryar, domin cewa shi bai san a'ina hannunsa ya kasance ba, ba zai iya amintar da najasa akan su ba, zai iya yiwuwa Shaidan ya yi wasa da su kuma ya dora abubuwa masu cutarwa garesu ga mutum ko mai bata ruwan.