Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya kwanta dan yayi barci, sai ya shimfiɗa hannunsa na dama kuma ya sanya kundukukinsa (kumatunsa)na dama akansa, sai ya ce: «Ya Allah» Ubangijina «Ka kareni» Ka kiyayeni daga «azabarKa» da uƙubarKa «ranar da zaKa tara ko zaKa tashi bayinKa» a ranar hisabi, ranar alƙiyama.