Ya kasance daga shiriyarsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - idan ya zo wa shinfidarsa dan ya yi bacci yana tara tafikansa biyu sai ya daga su - kamar yadda mai addu'a yake yi - sai ya yi tofi a cikinsu daga bakinsa sassaukan tofi tare da yawu sassauka sai ya karanta surori uku: {Ka ce Shi ne Allah Shi kadai} da {Ka ce ina neman tsari da Ubangijin safiya} da {Ka ce ina neman tsari da Ubangijin mutane}, sannan ya shafi abinda zai yi wu daga jikinsa; yana mai farawa da kansa da fuskarsa da bangare na gaba daga jikinsa, yana maimaita wannan aikin sau uku.