An tambayi Umar Dan Khaddab -Allah ya yarda da shi- ya tambayi Annabi -tsira da aminci su tabbata a gare shi: Idan janaba ta sami wani tun farkon dare ta hanyar saduwa da iyali ko mafarki, shi zai iya kwanciya bacci a haka? sai Mai tsira da amincin Allah ya basu damar yin haka amma idan anyi alwalla irin ta salla.