Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya yi nufin shiga gurin da zai biya bukatarsa a cikinsa, fitsarine ko bayan gida, zai nemi tsarin Allah, kuma zai fake gareShi da ya kareShi daga sharrin Shaidanu maza da mata, An fassara khubs da kahaba'is kuma da sharri da kuma najasa.