Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana wasu ladubba; yayin da ya hana mutum ya riƙe azzakarinsa a halin fitsari da hannunsa na dama, ko kuma a gusar da najasa daga gaba ko baya da hannun dama; domin dama an tanadeta ne dan manyan abubuwa, kamar yadda ya yi hani mutum ya yi numfashi a cikin ƙwaryar (kofi) da yake sha acikinta.