explain-icon

Bayani

Umar Dan Abu Salama - Allah Ya yarda da su - ɗan matar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - Ummu salamah - Allah Ya yarda da ita - yana ba da labari - (cewa) ya kasance ƙarƙashin renonsa da kulawarsa -, cewa ya kasance a tsakiyar cin abinci yana yawo da hannunsa asasannin ƙwarya (kwanon abin ci) don ya ɗauki abincin, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya sanar da shi ladubba uku daga ladubban cin abinci. Na farkonsu: Faɗin "Da sunan Allah" a farkon ci. Na biyunsu: Cin abinci da dama. Na ukunsu: Cin abinci daga ɓangaren da yake kusa daga gare shi na abincin.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Daga ladubban ci da sha (akwai) ambaton Allah a farkonsa.
  • Sanar da yara ladubba, musamman ma waɗanda ke ƙarƙashin kulawar mutum.
  • Tausayin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da yalwar ƙirjinsa a koyar da yara da ladabtar da su.
  • Daga ladubban abinci akwai cin abin da ke gaban mutum, sai dai idan ya kasance nau'uka ne da yawa, to, yana da damar da zai ɗauki wanda ya so.
  • Lazimtar sahabbai da abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ladabtar da su da shi, hakan abin fahimta ne daga faɗin Umar: Hakan bai gushe (irin) cin abincina ba bayan nan.