Wasu jama'a daga sahabban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sun zo sai suka tambaye shi game da abinda suke jinsa a cikin zuciyar su na manyan al'amuran da furta su zai girmama akansu saboda muninsu da kuma kyamarsu garesu. Sai tsira da aminci su tabbata agare shi ya ce: Lallai abinda kuke samunsa shi ne imani baro-baro da sakankancewar da zai kaiku ga hana abinda Shaidan yake jefawa acikin zuciya da kuma inkarinku ga furta shi, da girmama hakan acikin zukatan ku, kuma lallai cewa Shaidan ba ya samun dama a cikin zukatanku, sabanin wanda ya samu dama a zuciyarsa kuma bai samu abinda zai tunkude masa hakan ba.