Wani mutum ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbat agare shi - sai ya ce: Ya Manzon Allah, lallai dayanmu yana jin wani al'amari yana bijiro masa a zuciyarsa, saidai ya fade shi abu ne mai girma ne wanda ya kai matakin ace ya zama toka ya fi soyuwa agare shi akan ya fadeta. Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi kabbara sau biyu ya godewa Allah da ya mayar da kaidin Shaidan zuwa ga mujarradin wasuwasi.