Jabir ɗan Abdullahi - Allah Ya yarda ad shi - ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa a shekarar da aka buɗe Makka, alhali shi yana Makka: Lallai Allah da ManzonSa sun haramta saida giya da mushe da alade da gumaka, sai aka ce : Ya Manzon Allah, shin ya halatta mu saida kitsen mushe? domin su ana shafe jiragen ruwa da su, kuma shafe fatu da su, kuma mutane suna kunna fitilunsu da su, sai ya ce: A'a, saida su haramun ne, sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce a wannan lokacin: Allah Ya halakar da Yahudawa kuma Ya la'ancesu; lallai Allah yayin da Ya haramta musu kitsen dabbobi sai suka narkasu, sannan suka saida mansu suka ci kuɗinsa.