Daga Abdullahi Bn Umar -Allah ya yarda da su- ya ce: Manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "An halatta muku Matattu guda biyu da jini guda biyu, amma Matattun sune Kifi da Fara, kuma Jinin shi ne Zuciya da Hanta"
Ingantacce ne - Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi