explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani daga cin dukkan zakuna daga dabbobin masu farauta waɗanda suke farauta ta hanyar hakoransu, da kuma cin dukkan tsuntsun da yake yankewa kuma yake kamu da faratansa.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Kwaɗayin musulunci akan abubuwa tsarkaka na halas a cikin kowane abu daga abubuwan ci da abubuwan sha da wasunsu.
  • Asali, a cikin abubuwan ci shi ne halacci; sai abinda dalili ya yi nuni akan haramcinsa.