explain-icon

Bayani

Nana Asma'u tana Bada labarin cewa sun soke doki a lokacin Annabi kuma sun ci namansa, kuma cikin hakan akwai Dalilai kan Halaccin cin Naman doki kuma babu wanda zai kasa gane halacin hakan don kawai an hada ambatonsu da Jaki da Alfadari a ayar da take cewa: "Kuma doki da Alfadari da Jaki duk don ku haune kuma kuyi Ado kuma Allah yana halittar wasu Abubuwan da baku sani ba" [Annahl: 8].