Rafi'i ɗan Khadij - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa su sun kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a Zul-Hulaifa, sai yunwa ta kama mutane, alhali sun samu ganimar raƙuma da tumakai daga mushrikai, sai suka yi gaggawa kafin raba ganima sai suka yanka wasu daga cikinsu, kuma suka kafa tukwane, ba tare da sun nemi izinin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ba, kuma (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana tafiya a cikin ƙarshen mutane, lokacin da (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya sani sai ya yi umarni da tukwanan, sai aka kifar da su da abinda ke cikinsu na miya, sannan ya raba ganimar a tsakaninsu, sai ya sanya goma daga cikin tumakai a madadin rakumi daya, sai wani rakumi ya gudu daga cikinsu, sai suka kasa kama shi, kuma dawakan sun kasance kada ne, sai wani mutum ya harbe shi da kibiya, sai Allah Ya tsare musu shi, sai (Annab) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Lallai akwai wasu ɗabi'u kamar ɗabi'un daji ga waɗannan dabbobin masu sabo, wanda ya rinjayeku daga cikinsu kuma kuka kasa kama shi to ku yi haka da shi. Sai Rafi'u ya ce: Lallai mu mana fatan fuskantar maƙiya gobe, kuma muna jin tsoron yankanmu ga dabbobin ya cutar da makamanmu alhali ana tsananin buƙatar yanka, kuma babu wuƙa a tare da mu, shin zamu yanka ne da busassun karare? Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Duk abinda ya zubar da jini kuma ya kwaranyar da shi da yawa, kuma aka ambaci sunan Allah a kansa to ku ci shi, banda haƙori da farce, kuma zan zantar daku game da hakan: Amma haƙori to ƙashi ne, amma farce to mutanen Habsha kafirai ne suke amfani da shi.