explain-icon

Bayani

Anas - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yanka raguna biyu wato mazan tumakai, masu fararen ƙahunhuna waɗanda baƙi ya cakuɗa da su, kuma ya ce: Da sunan Allah, Allah ne Mafi girma, kuma ya ɗora ƙafarsa akan wuyansu.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Halaccin layya, haƙiƙa musulmai sun haɗu akanta.
  • Abin da ya fi layya ta zama daga wannan nau'in da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi layya da shi; dan kyan ganinsa da kuma kasancewar kitsensa da namansa yafi daɗi.
  • AlNawawi ya ce: A cikinsa cewa an so mutum ya jiɓinci yanka layyarsa da kansa, kada ya wakilta a yankata sai da wani uzuri, a wannan lokacin an so ya halacci yankanta, idan ya wakilta wani musulmi ya halatta babu wani saɓani.
  • Ibnu Hajar ya ce: A cikinsa akwai son kabbara tare da basmala a lokacin yanka da son ɗora ƙafar dama akan fatar wuyan abin layyar, kuma sun haɗu akan cewa kwantar da ita yana kasancewa ne a ɓangaren hagu sai ya ɗora ƙafaresa akan ɓangaren dama dan ya zama ya fi sauƙi ga mai yankan a wurin riƙe wuƙa da dama, da riƙe kanta da hannunsa na hagu.
  • An so layya da mai ƙaho kuma yana halatta da waninsa.