Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya bai wa sahabbai labari da samun nasarar musulmai akan Yahudawan Khaibara a wayewar gari, hakan ta hannun wani mutum da zai ba shi tuta ne alamar da runduna take rikewa alama a gare ta. Wannan mutumin daga siffofinsa cewa shi yana son Allah da manzonSa, kuma Allah da manzonSa suna sonsa. Sai sahabbai suka kwana suna tunani suna tattaunawa ga wanda za'a bai wa tutar? dan kwaɗayin wannan matsayi mai girma, Lokacin da gari ya waye sai suka tafi zuwa wurin manzon Allah - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - kowannensu yana kwaɗayin ya rabauta da wannan matsayin, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi tambaya game da Aliyu ɗan Abu Dalib - Allah Ya yarda da shi -? sai aka ce : Lallai ba shi da lafiya, yana fama da ciwon idanunsa. Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya aika a zo masa da shi, sai ya yi tofi a idon (sayyidina) Aliyu daga yawansu mai daraja, kuma ya yi masa Addu’a, sai ya warke daga cutar kai kace babu wani ciwo a tare da shi, sai ya ba shi tuta, kuma ya umarce shi da zarcewa cikin sauƙi har sai ya yi kusa daga ganuwar maƙiya sai ya bijiro musu da shiga musulunci, idan sun amsa masa; sai ya ba su labari da abinda yake wajaba akansu na farillai. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya bayyanawa Aliyu falalar kira zuwa ga Allah, kuma mai Da'awah idan ya zama sababi a cikin shiriyar wani mutum ɗaya to hakan shi ne mafi alheri a gare shi da ya samu jajayen raƙuman da su ne mafi tsadar dukiyoyin Larabawa, sai ya mallakesu ko ya yi sadaka da su.