A cikin kowace Al-umma daga cikin Al-ummai wani Mutum da ya shahara da Amana sama da kowa, kuma mafi Shaharar wannan Al-ummar da Amana shi Abu Ubaidah Amir Bn Al-jarrah -Allah ya yarda da shi- saboda shi koda yake amanar ta kasance sifa ce da kowa daga cikin sahabbai yayi tarayya da shi a cikinta -Amincin Allah ya tabbata a gare su- sai sigar Hadisin tana nuna cewa ya xaresu a cikinta