Tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi ya yi hani daga bakance, shi ne mutum ya wajabtawa kansa wani abu wanda shari'a ba ta wajabta masa ba, kuma ya ce: Lallai bakance ba ya gabatar da komai kuma ba ya jinkirtar da shi, kawai ana fitar da shi ne daga marowacin da ba ya aikata komai sai wajibin da ke kansa kawai, kuma bakance ba ya zuwa da abinda ba'a kaddara masa shi ba.