Annabi tsira da amincin Allah su tabba a gare shi, yana bayyana ayyuka na ƙwarai a goman farko na watan and Zul Hijja (Watan babbar Sallah) ya fi a kan sauran kwanakin shekara. Sahabbai Allah ya yarda da su, suka tambayi Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi dangane da Jihadi a kwanakin da ba waɗannan goman ba, shin shi ne ya fi ko kuwa ayyuka na ƙwarai a waɗannan kwanakin? saboda abin da suka sani na Jihadi yana cikin mafificin ayyuka. Sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya amsa da cewa kyawawan ayyuka a waɗannan kwanakin sun fi Jihadi a wasu kwanakin, sai dai mutumin da ya fita yana mai Jihadi da kutsawa hatsari da ransa da dukiyarsa; Don ɗaukaka addinin Allah sai ya rasa dukiyar ta sa kuma ran shi ya fita domin ɗaukaka addinin Allah. To wannan shi ne ya fi a kan aiki na ƙwarai a cikin waɗannan kwanaki masu falala.