A cikin wannan Hadisin Akwai bayanin Falalar Allah Madaukakin Sarki ga bayinsa a lokacin da suka sauke Nauyin Ibadu Saboamar yadda ake basu lada lokacinj tafiya zuwa gareta; haka ake basu lada lokacin da suke dawowa ma daga sauke ta, don haka Annabi ya bada Labarin cewa Mai dawowa daga Yaki kamar Mai tafiya yakin ne, kuma daidai suke a wajen lada, Kamar yadda ake rubuta takun Mai tafiya Masallaci da kuma dawowarsa zuwa iyalansa.