explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa wanda ya nemi shahada da mutuwa a tafarkin Allah, kuma ya kasance mai gaskiya mai tsarkake niyyarsa ga Allah - Mai girma da ɗaukaka -, Allah Zai ba shi darajojin shahidai saboda niyyarsa ta gaskiya koda ya mutu akan shinfiɗa ba a yaki ba.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Gaskiyar niyya tare da aikata abin da za'a iya, sababi ne na samun abin nufi na lada da sakamako, koda bai yi aikin da ake nema ba.
  • Kwaɗaitarwa akan jihadi da neman shahada a tafarkin Allah - Mai girma da ɗaukaka -.
  • Baiwar Allah - Mai girma da ɗaukaka - ga wannan al'ummar, shi (Allah) yana bada mafi ɗaukakar darajoji a cikin aljanna da kankanin aiki.