Daga Abu Hurairah, Allah ya yarda da shi, ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Mutumin da ya yi kuka saboda tsoron Allah ba zai shiga wuta ba har sai madara ta dawo a cikin nono, kuma babu tarin kura saboda Allah da hayakin Jahannama." Ingantacce ne - Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Al-Nasa'i Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi