explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda ya tanadarwa wani mayaki a tafarkin Allah sabubban tafiyarsa da abinda yake bukatuwa gare shi daga abinda babu makawa gare shi na makami da abin hawa, da abinci, da ciyarwa da waninsu; to shi yana cikin hukuncin mai yin yaki, kuma ladan mayaki zai same shi . wanda ya jibinci al'amarin mayaki da alheri, kuma ya maye gurbinsa a cikin kula da iyalansa a lokacin da ba ya nan to shi yana cikin hukuncin mayaki yake.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Kwaɗaitar da musulmai akan taimakekeniya akan ayyukan alheri.
  • Ibnu Hajar ya ce: A cikin wannan Hadisin a kwai kwaɗaitarwa akan kyautatawa ga wanda ya aikata wata maslaha ga musulmai, ko ya tsaya da wani al'amari daga abubuwan da ya shafesu.
  • Ka'ida gamammiya: Cewa wanda ya taimaki wani mutum a cikin aikin ɗa'a daga ayyukan ɗa'a ga Allah to yana da kwatankwacin ladansa, ba tare da an rage wani abu daga ladansa ba.