explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi albishir da cewa wanda ƙura ta samu diga-digansa alhali shi yana yaƙi a tafarkin Allah cewa wuta ba zata shafe shi ba.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Albishir ga mai yaƙi a tafarkin Allah da tsira daga wuta.
  • Ya ambaci diga-digai duk da cewa ƙura tana game dukkan jiki; domin cewa mafi yawancin mayaƙa a wancan zamanin masu tafiyar ƙasa ne, diga-digai kuwa suna ƙura akowane hali.
  • Ibnu Hajar ya ce: Idan mujarradin taɓa ƙura ga diddige yana haramta masa wuta; to ta yaya ga wanda ya yi ƙoƙari iya ƙoƙarinsa ya ƙarar da ƙarfinsa.