Wadannan hadisai biyu suna nuna mana falalar yin jihadi don Allah koda kuwa dan kadan ne gwargwadon lokacin safiya ko na yamma, ballantana kuma lokaci mai yawa wanda cikinsa akwai tsananin hakuri da gwagwarmaya da abokan gaba, wannan shi ake nufi da yi don Allah, watau yakar kafirai. Kuma ya kamata asan cewa neman ilmin sharia shina bangare ne mai girma na jihadi don Allah, hakanan taimakon gaskiya, hakanan ruguza hujjojin zindikai arna turawa yanmishan masu yakar musulumci masu son gani bayansa shi ne mafi girma cikin jihadi a tafarkin Allah. Manufar jihadi, shi ne bayyana Musulunci da taimaka masa, kuma dakushe arna, yana daga jihadi mai girma. Ya Allah ka datar da Musulmi a wajen taimakawa addininsu, da daukaka kalmarka. Kai ne Makusanci Mai amsawa.