Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa lazimtar gurin da yake tsakanin musulmai da kafirai dan gadin musulmai daga gare su a yini ɗaya yana mai tsarkake niyya saboda Allah, shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke cikinta, kuma bigiren bulalar da zai yi yaƙi da ita saboda Allah a cikin aljanna shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke cikinta, kuma lallai cewa lada da sakamakon tafiya a cikin lokaci daga farkon yini zuwa farkon lokacin azahar, ko yammaci: Daga lokacin azahar zuwa dare saboda Allah sau ɗaya, shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke cikinta.