explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa babu wani mutum daga mutane da zai ketare matsayar hisabi a ranar Alkiyama zuwa aljanna ko wuta ba har sai an tambaye shi game da wasu al'amura: Na daya: Rayuwarsa a me ya karar da ita? Na biyu: Iliminsa shin ya neme shi ne saboda Allah? kuma ya yi aiki da shi? kuma shin ya isar da shi ga wanda ya cancance shi? Na uku: Dukiyarsa daga ina ya samota shin daga halal ne ko daga haram? kuma a me ya ciyar da ita a abinda zai yardar da Allah ne, ko a abinda zai fusatar da Shi? Na hudu: Jikinsa da karfinsa da lafiyarsa da samartakarsa a me ya yi da shi ya kuma aiwatar da shi?

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Kwadaitarwa akan ribar rayuwa a cikin abinda zai yardar da Allah - Madaukakin sarki -.
  • Ni'imomin Allah ga bayinSa masu yawa ne kuma za'a tambaye shi daga ni'imar da ya kasance a cikinta, to ya wajaba akansa ya sanya ni'imomin Allah a abinda zai yardar da Shi.