Dan Abbas yana Fassara wannan Aya mai girma cewa wadan nanGumakan wadanda aka ambata a Alkurani cewa Mutanen Annabi Nuhu ne sunyi ta yiwa junansu wasiyya da ayi ta bauta musu bayan Annabinsu ya hanasu ga barin yin Shirka da Allah, kuma cewa ita a Asali sunaye ne na Mutanen kirki daga cikinsu, wanda suka wuce gona da Iri da yadda Shaidan ya kawata Musu har suka kafa gumakansu, sai kuma al'amarin wadan Hotunan ya koma Gumaka da ake bauta musu koma bayan Allah.