explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bada labarin cewa wanda ya yi rantsuwa da wanin Allah da sunayensa da siffofinsa to hakika ya kafircewa Allah ko ya yi shirka; domin rantsuwa tana hukunta girmama wanda aka rantse da shi, girma kadai ya tabbata ga Allah ne Shi kadai; ba'a rantsuwa sai da Allah da sunayensa da siffofinsa - tsarki ya tabbatar masa, Wannan rantsuwar tana daga karamar shirka; saidai da a ce mai rantsuwa ya girmama abinda ya rantse da shi kamar girmama Allah - Madaukakin sarki - ko sama da haka; to a wannan lokacin zai zama daga babbar shirka.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Lallai cewa girmamawa da yin rantsuwa hakki ne na Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya daukaka - ba'a rantsuwa sai da Allah da sunayenSa da siffofinSa.
  • Kwadayin sahabbai akan horo da aikin alheri da kuma hani daga abin ki, musamman ma idan abin kin ya kasance daga abinda yake rataya ne da shirka ko kafirci.