yayin da wannan Sahabin mai girma yaji karatun Manzon Allah-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-na wannan ayar wacce ta kunshi labarin yahudu da nasara:cewa sun mayar da malamansu da masu ibadar cikinsu abin bauta,suna shar'anta musu abinda yasabawa shari'ar Allah kuma suyi musu biyayya a kan haka,to sai ma'anar ayar ta rikitar,domin shi sahabin ya zaci cewa bauta ta takaita akan yin sujjada da makamantanta,sai Manzo -tsira da amincin Allah-ya bayyana masa cewa yana daga bautawa malamai yi musu biyayya a wajan haramta halal da kuma halarta haram,sabanin hukunci Allah madaukaki da Manzonsa tsira da aminci su tabbata a gare shi