explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya roki Ubangijinsa da kada Ya maida kabarinsa tamkar gunkin da mutane suke bauta masa ta hanyar girmama shi, da fuskantarsa a cikin sujjada, sannan tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya sanar da cewa Allah Ya nisantar Ya kore wanda ya maida kaburburan Annabawa masallatai daga rahamarsa' domin maida su masallatai sila ce zuwa bauta musu da kuma kudircewa a cikinsu.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Ketare iyaka ta shari'a a cikin kaburburan Annabawa da salihan bayi ya maida su ana bauta musu koma bayan Allah, to kiyayewa daga hanyoyin shirka ya wajaba.
  • Nufin kaburbura dan girmama su ba ya halatta da kuma yin ibada a gurin su duk yadda kusancin masu su yake ga Allah - Madaukakin sarki -.
  • Haramcin gina masallatai akan kaburbura.
  • Haramcin sallah a wurin da kaburbura suke koda bai yi gini ba saidai sallar jana'izar da ba'a yi wa gawar sallah ba kadai.