Uwar muminai Ummu Salama - Allah Ya yarda da ita - ta fadawa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa ta kasance a kasar Habasha ta ga wata coci - ana ce mata Mariya - a cikinta akwai hotuna da kawace- kawace da zane-zane; dan mamaki daga hakan! Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana dalilan sanya wadannan hotunan; Sai ya ce: Wadannan wadanda kike fada sun kasance idan mutum nagari ya mutu a cikinsu, sai su gina masallaci akan kabarinsa suna sallah a cikinsa, su kuma zazzana wadancan hotunan, ya bayyana cewa mai aikata wancan shi ne mafi sharrin halitta a wurin Allah - Madaukakin sarki -; domin aikata shi yana kaiwa zuwa shirka da Allah - Madaukakin sarki -.