Wanda camfi ya mayar da shi ga barin bukatarsa; to hakika ya yi shirka suka ce menene kaffarar hakan? ya ce: Ka ce ya Allah! babu wani alheri sai alhairinka, kuma babu camfi sai dai abin da ka nufa, kuma babu abin bauta da cancanta in ba kai ba Ingantacce ne - Ahmad ne ya rawaito shi