Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi umarnin yawan maimaita Alƙur’ani da dagewa a kan karanta shi; domin kada a manta bayan an haddace shi a zuciya, [Annabi] tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kuma ƙarfafi hakan da rantsuwa a kan Alƙur’ani ya fi saurin ɓacewa da tafiya daga zuciya a kan raƙumi da aka ɗaure, ga shi a ɗaure da igiya a ƙwauri, idan mutum yana yawan bibiyarsa sai ya riƙeshi, idan kuma ya sakeshi sai ya tafi ya ɓace.