Nu'uman ɗan Bashir - Allah Ya yarda da su - ya bada labarin cewa mahaifiyarsa Amrah 'yar Rawaha - Allah Ya yarda da ita - ta tambayi babansa wata kyautar da zai bawa ɗanta daga dukiyarsa, sai ya yi nauyi ya jinkirtata har shekara, sannan ya ga ya kamata ya amsa mata abinda ta nema sai ya bawa ɗansa Nu'uman kyauta, sai ta ce: Ba zan yarda ba har sai ka sa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sheda akan abinda ka bawa ɗana, sai babana ya riƙe hannuna ni kuma a wannan lokacin ina ƙaramin yaro, sai ya zo wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce: Ya Manzon Allah, lallai cewa babar wannan 'yar Rawaha tana son in sakaka shaida akan abinda na bawa ɗanta kyauta, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Ya kai Bashir, shin kana da wani ɗan ne banda wannan? Ya ce: Eh. Sai ya ce: Shin dukkansu ka ba su kwatankwacin wannan? Ya ce: A'a. Ya ce: To kada ka sa ni shaida, domin cewa ni ba na shaida a kan zalinci. A riwayar Muslim ya ce yana mai zarginsa: Sai dai ka sa wanina ya yi shaida a kan wannan zalincin.