Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin halin Shaiɗan da kuma yakinsa ga mutumin da yake nufin tsayuwa dan sallar dare ko Asuba. domin mumini idan ya tafi yin bacci shaiɗan yana ƙulli uku akan ƙyaraysa - yana nufin: Ƙarshen kansa -. Idan mumini ya farka kuma ya ambaci Allah - Maɗaukakin sarki - bai amsa waswasin shaiɗan ba; sai ƙulli (ɗaya) ya warware. Idan ya yi alwala sai ya warware. Idan ya tashi ya yi sallah sai ƙulli na uku ya warware, sai ya wayi gari mai yawan nishaɗi mai daɗin rai; dan farin cikinsa da abinda Allah Ya datar da shi na aikin ɗa'a, yana mai bushara da abinda Allah Ya yi masa alƙawari na lada da gafara, tare da abinda ya gushe daga gare shi na ƙulle-ƙullen Shaiɗan da nauyayawarsa, in ba haka ba zai wayi gari mai mummunan rai, mai baƙin ciki a zuciya, mai kasala daga ayyukan alheri da biyayya; domin cewa shi abin ɗaurewa ne da marin Shaiɗan, kuma abin nisanta daga kusancin Al-Rahman.