Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da ambatan Allah a yayin shiga gida da kafin cin abinci, kuma cewa shi idan ya ambaci Allah da fadinsa: (Da sunan Allah) a lokacin shigarsa da kuma lokacin fara abincinsa, Shaidan zai cewa mataimakansa: Baku da rabo na makwanci ko abincin dare a wannan gidan da mai shi ya kare kansa daga ku da ambatan Allah - Madaukakin sarki -. Amma idan zai shiga gidansa bai ambaci Allah a lokacin shigarsa ba ko lokacin cin abincinsa, sai Shaidan ya sanar da mataimaknsa cewa sun sami makwanci, da abincin dare a wannan gidan.